Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar ISIS Ta Yiwa Wani Dan Kasar Rasha Yankan Rago a Syria


ISIS

Kungiyar tsageran ‘yan tawayen IS ta fito da wani faifan bidiyo jiya Litinin da dare, inda take nuna suna yi wa wani ma’aikacin leken assirai na Rasha yankan rago a Syria.

IS tace abinda ta nuna shine yadda ta yanka Capt. Yevgeny Petrenko, 36, wanda kungiyar ta zarge shi da laifin cewa ya kutsa kansa cikin rassanta dake yankin Caucus na arewancin Rasha.

Sai dai kuma, a cewar kafofin watsa labaran Rasha, tuni ma’aikatar Tsaron kasar ta musanta cewa mayakan IS sun taba kama ko daya daga cikin ma’aikatanta.

Mutumen da akace shine Petrenko a cikin bidiyon, yace gwamnatin Rasha ce ta aika shi don yayi shigar burtu, ya shiga cikin kungiyoyin, ya ga irin wainar da shugabanninta ke toyawa.

Haka kuma ya zargi Hukumar Tsaro ta Rasha da cewa ta juya mishi baya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG