Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Izala Ta Kai Tallafi Gidan Kason Yola


Musulmai a Najeriya

Yayin da take cigaba da taimakon marasa karfi cikin wannan wata mai albarka kungiyar Izala ta kai tallafi gidan kason Yola

A kokarinta na cigaba da aikin jin kai cikin wannan wata mai albarka, kungiyar Izala to kaima wadanda suke gidan kaso a Yola tallafi.

Yayin da yake yima firsinonin addua Sheikh Kabiru Gombe ya roki Allah ya yafe masu zunubansu, ya bude masu hanya,ya sa su zama manyan 'yan kasuwa da masana Kur'ani. Su dai 'yan kason kusan kashi casa'in matasa ne da suka aika laifuka daban-daban.

Da dama cikin 'yan kason sun dade a tsare suna jiran a yi masu hukunci. Wasu sun kwashe fiye da shekaru goma ba'a yi masu sharia ba kuma ba'a sake su duk da cewa wasu laifukansu basu taka kara sun karya ba. A jawabinsa shugaban kungiyar Izala Alhaji Abdullahi Bala Lau ya yi mamakin yadda za'a tsare mutum a gidan kaso shekara da shekaru ba tare da yimas shari'a ba. Ya kira mahukunta su ji tsoron Allah. Tsare mutum a gidan kaso ba hukunci tamkar zalunci ne.

Sarkin matasan Adamawa Abdulaziz Murtala Nyako ya yi alkawarin taimakawa a saki wadanda suka dade kuma laifinsu ba wani laifin kirki ba ne. Amma ya gargadesu su yafewa wadanda suka yi sanadiyar tsaresu, su gyara halayensu domin kada su sake shiga irin wannan halin.

Da alamu 'yan kason sun yi nadama kuma a shirye suke su yi rayuwar kwarai idan suka samu 'yanci.

Ibrahim Abdulaziz nada rahoto.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:57 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG