Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Hada kan Kasashen Larabawa Ya yi Sassauci Kan Shawarwarin Sulhu Da Isra'ila.


Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry daga hagu,da PM Qatar Sheikh Hamad bin Jassim al-Thani shima daga hagu, a wani taro da tawagar kungiyar hada kan kaashen larabwa, da suka yi anan Washington.

Wata tawagar manyan jami’an kungiyar hada kan kasashen larabawa, ta bayyana goyon baya ga manufofin shawarwari tsakanin Isra’ila da Falasdinu.

Wata tawagar manyan jami’an kungiyar hada kan kasashen larabawa, wacce take ziyarar aiki anan Washington ahalin yanzu, ta bayyana goyon baya ga manufofin shawarwari tsakanin Isra’ila da Falasdinu da zai kunshi musayar muhallai a kokarin shata kan iyakoki tsakanin kasashen, nan gaba.

Bayan ganawarsa da sakataren harkokin wajen Amurka a wani masaukin gwamnatin Amurka da ake kira Blair House jiya litinin, PM Qatar yace tawagarsa tana goyon bayan musayar muhallai wadanda girmansu kusan daya ne tsakanin sassan dake gardama da juna.

Furucin PM Qatar Sheikh Hamad Bin Jassem Al Thani, alama ce ta sassauci kan matsayr kungiyar na shekara da shekaru dangane shawarwarin sulhu tsakanin Isra’ila da Falasdinu. Kudurin kungiyar na shekara da shekaru shine na bukatar Isra’ila ta janye daga dukkan muhallan kasashen larabawa data mamaye bayan yakin da ta gwabza da su a 1967, idan Isra’ilar ta yi haka to kasashe dake cikin kungiyar baki daya zasu maida huldar jakadanci da Isra’ila.

Wannan sabon matsayar kungiyar tamkar amincewa ce ga sharuddan wanzarda zaman lafiya da shugaban Amurka Barack Obama ya gabatar a 2011, wanda ya bukaci Isra’ila da yankin Falasdinu da su yi shawarwarinsu tare da la’akari da kan iyakokin kamin yakin 1967, wanda zai hada da musayar muhallai.
XS
SM
MD
LG