Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Kasashen Larabawa Ta Damu da Kudirin Majalisar Dokokin Amurka


Shugabannin Saudiya da Sakataren Harkokin Wajen Amurka
Shugabannin Saudiya da Sakataren Harkokin Wajen Amurka

Majalisar dokokin Amurka ta amince da wani kuduri da ya baiwa iyalan wadanda suka rasa rayukansu sanadiyar harin ta'adancin shekarar 2001da al-Qaida ta kai kan Amurka su gurfanar da kasar Saudiya gaban shari'a domin neman diya

Kungiyar Kasashen Larabawa dake yankin Gulf, ta nuna damuwarsu kan wani kudiri da Majalisar Dokokin Amurka ta amince da shi, wanda zai baiwa iyalan wadanda suka mutu a harin ranar 11 ga watan Satumbar shekarar 2001, su shigar da gwamnatin Saudiyya kara, bisa zargin sun marawa aikin ta’addancin baya.

Kungiyar mai mabobi shida a Majalisarta, wacce Saudiyya babbar mamba ce, ta ce kudirin da Majalisar dokokin Amurkan ta amince da shi, ya sabawa ka’idojin kawance da ke tsakanin kasashen.

A ranar Juma’ar da ta gabata ne, majalisar wakilan Amurka ta amince da wannan kuduri, duk da barazanar da Fadar White House ta yi na cewa za ta yi amfani da karfin da doka ta bata domin yin watsi da kudurin.

Ita dai Majalisar Dattawan Amurka tun a watan Mayu ta amince da wannan kuduri, wanda zai ba da damar hukunta mai daukar nauyin ayyukan ta’addanci.

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG