Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Kwadago NLC Za Ta Shiga Yajin Aiki Saboda Karancin Kudi A Najeriya


Tambarin Kungiyar Kwadago ta Najeriya NLC
Tambarin Kungiyar Kwadago ta Najeriya NLC

Kungiyar kwadagon Najeriya NLC za ta fara gagarumin yajin aiki daga ranar laraba mai zuwa don nuna fusata da yanda gwamnati ta kasa wadatar da ma'aikata da takardun kudin da za su rika yin cefane.

Shugaban kungiyar Kwadago ta NCL, Komred Joe Ajero ne ya sanar da umurnin a taron kungiyar a Abuja.

Shugaban kungiyar kwadago NLC Kwamared Joe Ajero
Shugaban kungiyar kwadago NLC Kwamared Joe Ajero

Sakamakon taron ya nuna kungiyar ta gaji da bukatar da ta mikawa babban bankin Najeriya CBN, da ya wadatar da kudin amma sai kara ta'azzara lamarin ya ke yi.

Sakataren tsare-tsare na kungiyar Komred Nasir Kabir ya ce 'yan kungiyar za su mamaye ofisoshin babban bankin, kuma an umurci ma'aikata su zauna a gida.

In za a tuna hukuncin kotun koli na yin amfani da tsoffin kudi tare sa sabbi ne ya dan sauya lamura, inda gwamnatin bayan jan kafa ta mika wuya don gudun kar a ci gaba da sukar ta cewa ba ta bin umurnin kotu.

Wata matsalar ita ce ta dan karen tsada da karancin man fetur, inda farashin ke bambanta daga nan zuwa can.

An sayar da litar Man Fetur akan Naira 320 a Jihar Nasarawa
An sayar da litar Man Fetur akan Naira 320 a Jihar Nasarawa

Yanzu dai za a jira a ga zafin da yajin zai yi a daidai lokacin da musulmi ke shiga azumin watan Ramadan.

Ga rahotan Nasiru Adamu El-Hikaya:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:21 0:00

XS
SM
MD
LG