Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Malaman jami’a Ta Ce Sojoji Sun Shara Karya.


Malaman jamiaar Maiduguri sunce jamiaan tsaro sun shara karya domin sun sanar da duniya cewa sun kwato mutanen da 'yan Boko Haram suka yi garkuwa dasu ashe matattu suka kwato.

Kungiyar Malamai jami’a reshen Maiduguri sun bayyana alhinin su game da rasuwar wasu abokan aikin su da aka kashe sakamakon kwanton bauna da ‘yan kungiyar Boko Haram tayi musu.

Da yake Magana da wakilin Sashen Hausa, Haruna Dauda Biu, shugaban kungiyar Malaman Dr. Daniel Mamman yace yana mika taaziyar kungiyar ga iyaye da ‘yan uwan wadanda wannan lamari ya rutsa dasu.

Yace wannan abu da ya faru basu kadai ne zasu ji da wannan bakin cikin ba, har da suma abokan aikin su.

Dr Daniel yace fatar su ita ce su wadanda har yanzu ba a san halin da suke ciki ba,ALLAH ya bayyanar dasu kuma cikin koshin lafiya.

Su kuma wadanda suka riga mu ALLAH ya jikan su

Ga Haruna Dauda Biu da Karin bayani 3’07

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:06 0:00

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG