Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar masu canjin kudade a Nigeria sun koka


Dan canji

Kungiyar masu Canjin kudaden kasashen ketare sun koka game da sabbin matakan hada hadan kudaden kasashen waje da Babban Bankin Kasa na CBN ya fitar

Kungiyar masu Canjin kudaden kasashen ketare sun koka game da sabbin matakan hada hadar kudaden kasashen waje da Babban Bankin Kasa na CBN ya fitar.

Matakan sun bukaci samun lambar BVN ga masu hada hadar kudaden ketare. Kungiyar ta fadawa wakilin sashen Hausa Babangida Jibirin cewa matakin nada hatsarin gaske.

A wani taron gaggawa da uwar kungiyar ta gudanar a birnin Lagos ranar Talata. Tace kodayake tana goyon bayan matakin gwamnati na dawo da darajar Naira, amma kuma wasu matakan baban Banki kamar na samun BVN yana saka tsoro a zuciyar masu mu'amala da kudaden kashen waje.

Alhaji Aminu Gwadabe,shine shugaban kungiyar masu saye da sayarwa na kudaden kasashen waje. Yace kimamin makoni biyu da suka shige baban bankin Nigeria ya zartar da abubuwa da dama, Ya zartar da abinda ya shafi yan canji da kuma wanda ya shafi yan kasuwa da kuma bankuna

Yace akwai bukatar kara wayarwa da yan canji da kuma jama'a kai dangane da lambar BVN

Wani mai hada hadar kudade yace tuni suka samu labarin cewa yan 419 sun sace lambar BVN, ke nan akwai rashin tsaro tattare da dashi. A saboda akwai bukatar ayi gyara

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:25 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG