Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Mata Mabiya Masahabar Shi’a Sunyi Zanga Zanga A Kaduna


Sheikh Zakzaky
Sheikh Zakzaky

A yayin da kwamnitin da gwamnatin jihar Kaduna ta kafa domin binciko musabbabin hayaniyar da ta tashi tsakanin mabiya darikar Shi’a a Zariya, da kuma rundunar sojan tarayyar Najeriya dake Kaduna. Wata kungiyar mata mabiya masahabar Shi’a tayi zanga zangar nuna damuwa a garin Kaduna.

Hajiya Lubabatu Alhassan Mohammad, daya daga cikin matan da sukayi wannan zanga zangar ta bayyana bukatar su, inda tace sun fitone domin nunawa Duniya cewa har yanzu fa jagoransu na hannun Sojojin Najeriya, bayan kashe rayukan mabiyar darikar da sojojin sukayi. Matan dai sun nemi a saki Mallam Ibrahim Zakzaki ba tare da wani sharadi ba.

Matan dai sunce basu yarda da kwamitin da gwamnati jihar Kaduna ta kafa ba, domin ba sa cikin wannan kwamiti kuma sun fada tun farko bazasu shiga ba har sai an saki jagoransu.

Sakataren kwamitin Dakta Bala Babaji, ya zanta da Muryar Amurka ranar da aka rantsar da su, har ya tabbatar da cewa zasu tsaya don ganin anyi adalci ga kowa.

Domin karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:47 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG