Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar NARTO Ta Dakatar Da Yajin Aikin Gamagari, Ta Umarci Ma’aikatan Ta Su Koma Bakin Aiki


Layin neman Mai a Yola
Layin neman Mai a Yola

Kungiyar ta janye yajin aikin da ta fara a jiya Litinin bayan shiga tsakani da gwamnatin tarayya ta yi tsakaninta da sauran masu ruwa da tsaki a fannin albarkatun man fetur kamar NNPCL, NMDPRA, DAPPMA da dai sauran su

Bayan shiga tsakanin da gwamnatin tarayyar Najeriya ta yi ta bangaren Hukumar Kula da Dokokin man fetur, da Karamin Ministan Albarkatun Man Fetur, Heineken Lokpobiri, kungiyar masu motocin dakon man fetur ta kasar wato NARTO, ta dakatar da yajin aikin gamagari da ta shirya daga jiya litinin 19 ga watan Fabrairun shekarar 2024 da muke ciki.

Da ga hagu: Faruk Ahmed da Heineken Lokpobiri
Da ga hagu: Faruk Ahmed da Heineken Lokpobiri

Wannan matakin dai ya biyo bayan ganawar da kungiyar da wasu masu ruwa da tsaki a fannin albarkatun man fetur suka fara daga jiya Litinin ya zuwa maraicen yau Talata.

Mambobin kungiyar NARTO dai sun dakatar da ayyukansu na jigilar man fetur a fadin kasar sakamakon tsadar man dizal da kuma matsin tattalin arziki a kasar.

Mambobin kungiyar NARTO sun yi barazanar tsayar da ayyukan su cir a fadin kasar tun daga jiya Litinin saboda tsadar man dizal wanda ake amfani da shi wajen jigilar man fetur da motocinsu a fadin Najeriya.

Masu ruwa da tsaki a fannin albarkatun man fetur
Masu ruwa da tsaki a fannin albarkatun man fetur

Kamar man fetur wanda a yanzu ake sayar da shi daga kan Naira dari 6 zuwa 7 kan kowace lita, farashin man dizal ya yi tashin gwauron zabi a musamman a baya-bayan nan, lamarin da ba ya rasa nasaba da tashin farashin dala a kasuwannin bayan fagge da na hukuma a kasar.

Shugaban NARTO, Yusuf Othman da wasu mahalarta taron.
Shugaban NARTO, Yusuf Othman da wasu mahalarta taron.

A yanzu dai ana sayar da man dizal sama da Naira dubu 1 da 250 akan kowace lita a Najeriya.

A saurari cikakken rahoton Halima Abdulrauf:

Kungiyar NARTO Ta Dakatar Da Yajin Aikin Gamagari
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG