Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana shakkun cewa Afghanistan Ba Zata Iya Daukar Alhakin Tsaron Kasar Ba


Dakarun kungiyar tsaro ta NATO
Wata kungiyar nazarin rikice rikice ta kasa da kasa da ake cewa ICG a takaice, wadda cibiyarta ke birnin Brussels kasar Belgium, tace, a yanzu gwamnatin kasar Afghanistan ba zata iya daukan alhakin kula da matakan tsaro idan sojoji Amirka dana kungiyar kawancen tsaro ta NATO suka janye a shekara ta dubu biyu da goma sha hudu ba.

Wannan kungiyar mai zaman kanta, tace gwamnatin Afghanistan zata wargaje, musamma idan aka tupka magudi a zaben da za’a yi a kasar nan gaba. A shekara ta dubu biyu da tara da kuma shekara ta dubu biyu da goma kasar tayi fama da rudami a zaben shugaban kasa dana Majalisar wakilan kasar da aka yi.

Rahoton kungiyar ICG da aka gabatar a jiya litinin yace, a yadda al’amurra suke a kasar a yanzu, yiwuwar gudanar da zabe ciki lumana zai yi wuya.

Wannan kungiya da cibiyarta ke birnin Brussels ta bada shawarar cewa ya kamata kasashen duniya su tabbata akwai shiri sosai na tabbatar da matakan tsaro a Afghanistan a lokacinda yakin neman zaben shugaban kasa a shekara ta dubu biyu da goma sha hudu. Haka kuma tayi kira ga jami’an zabe da wakilan Majalisar kasar da su daina yin kumbuya kumbuya, su magance batutuwan da suka danganci zabi, kafin ayi zaben.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG