Batun yau ba ne dai kungiyoyi na ciki da ma wajen Najeriya ke zargin dakarun sojin kasar da take hakkin bani Adama, batun da jami’an sojin kasar ke musantawa.
To sai dai a wani mataki inda gwamnatin Najeriya ta kafa wani kwamitin bincike kan take hakkin dan Adam da ake zargin sojoji da yi, za’a karbi bahasi daga kungiyoyi da kuma daidaikun jama’a da sojoji da 'yansanda amma ba tare da jin shugaban kungiyar ba Shaikh Ibrahin Yaqub El-Zakzaky wanda har yanzu yake tsare.
To sai dai yayin da kwamitin ke soma aiki, kungiyar yan uwa musulmi mabiya Sheikh Ibrahim ElZakzaky,wato IMN,dake zargin sojin kasar da kashe mata mabiya, na shakku tare da cewa ba za su halarci zaman kwamitin da ke binciken ba.
Arangamar dai ta faru ne bayan sojoji sun yi zargin cewa mabiya El Zakzakin sun tare hanyar da Babban Hafsan rundunar Sojin kasa na Najeriya, Laftanar Janar Yusuf Tukur Buratai ke kai a lokacin da ya kai ziyara garin Zaria a shekarar 2015, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama.
'Yan kungiyar dai sun ce sun dauki matakin ne sakamakon zargin da suke yi na cewa akwai abun dubawa game da kafa kwamitin. Mallam Ibrahim Musa shine shugaban dandalin yada labarai na kungiyar yan uwa Musulmin A Najeriya ya bayyana dalilansu na kauracewa hukumar binciken .
A har kullum dai rundunan sojin kasar cewa take dakarunta na aiki ne da kwarewa.Domin ko a zantawar da yayi da manema labarai a Yola kwanaki,kakakin rundunan sojin kasar Birgediya Janar Sani Usman Kukasheka,ya musanta zargin da kungiyoyin kare hakkin bani Adama ke yi.
Facebook Forum