Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Tarayyar Turai Ta Amince Ta Baiwa Girka Karin Kudi


Ministocin Kudi da na Tattalin Arzikin kasar Girka
Ministocin Kudi da na Tattalin Arzikin kasar Girka

Kungiyar tarayyar Turai ta amince da kara baiwa kasar Girka taimakon kudi bayan ta cika kaidodin da ta gindiya mata

A Turai, ministocin harkokin kudi na kasashe da suke cikin kungiyar sun amince a baiwa Girka dala miliyan dubu biyu da miliyan dari daya, a zaman wani bangare na yunkurin ceto kasar daga matsalolin tattalin arziki data shiga, bayan da hukumomi a Athens, suka zartas da wasu matakai na tilas da zummar yin garambawul ga tattalin arzikin kasar cikin makon jiya.

Jiya Litinin ne a hukumnce kungiyar ta EU ta amince da shirin, bayan da majalisar dokokin Girkan ta amince da sabbin matakai na tsuke bakin aljihu, da suka hada da karin kara kudin haraji,da haraji kan barasa, da kudin amfani da hanyoyi, da kuma takaita tallafin gwamnati da take baiwa wadanada suka gaza biyan kudin gidajen da suke ciki.

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG