Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Tsoffin Sojojin Nijar Ta Gargadi ‘Yayanta Su Guji Fadawa Tarkon ‘Yan Ta’adda


Taron tsoffin sojojin Nijar

Sabon salon da kungiyoyin ta’addanci suka fito dashi na daukan mayakan fada ya sa kungiyar dake kula da tsoffin sojojin kasar Nijar shirya taron fadakar dasu domin kada su fada tarkon kungiysr ISIS

Sakamakon lura da wasu bayanai dake fayyace shirin da kungiyoyin ta’addanci suka dukufa akansa a wannan lokacin da dakarun kasashen Sahel ke buga kirjin samun galaba akan ‘yan ta’adda, ya sa kungiyar tsoffin sojojin shirya wani taro na musamman domin fadakar dasu.

A taron, an gargadi tsoffin sojojin su nisanci kansu da wata sabuwar dabara da ‘yan ta’adda suka fito da ita.

Keften Yahuza Sabo mai ritaya yana cikin wadanda suka yi fadakarwar. A cewarsa yau kwadayin abun duniya ya yi yawa. Wanda yake son cutar kasar zai zo da wani tayi na masu “Shigo shigo ba zurfi”.Wasu na iya zuwa su yi masu tayin aikin gadi a wasu kasashen Asiyawa, amma daga bisani su samu kansu ko kuma su gane suna yiwa ‘yan ta’adda aiki.

Sabbin dabarun da ‘yan ta’adda suka fito dasu ya sa rundunar mayakan kasar Nijar suka ga akwai bukatar tsoffin sojoji su bada tasu gudummawa dangane da ayyukan tabbatar da tsaro ta hanyar dafawa askarawan dake fagen daga. Ana kuma ganin zasu iya taimakawa hukumomi a yankunan karkara akan maganar tsaro kamar yadda Keften Munkaila Abdullahi, daraktan kula da rayuwar tsoffin sojoji ya fada.

Keften Abdullahi y ace manyan kungiyoyin ta’addanci daga yankin Asiya sun aika da dillalai a kasashen Afirka da zummar neman masu aikin gadi a wasu kasashen nahiyar Asiya, sai dai an gano cewa shirin na da wata manufar boye, karkata masu gadin yin yaki a karkashin inuwar ISIS.

Masu sharhi akan al’amuran tsaro na cewa muddin ana son tabbatar da tsaro musamman a Afirka, ya zama wajibi kasashen su kula da tsoffin dakaru da wadanda suke aiki yanzu su kawar masu da kwadayi domin kada su fada tayin ‘yan ta’adda


Souley Barma nada karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:22 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG