Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyoyi Da Jamiyyun Siyasa A Tunisia Sunyi Kira Da Ayi Zanga-zanga.


Tunisia - a rally in support of the Ennahda ruling party in Tunis, 16Feb2013

Anaci gaba da gudanar da zanga-zangar nuna kin jinin gwamnati a kaar Tunisia, wanda akayi irin sa a shekaru 7 da suka gabata.

Kungiyoyi da jamiyyun siyasa a kasar Tunisia suna kira da a shiga wani sabon zanga-zanga yau lahadi.Bayan wanda aka kwashe tsawon sati guda anayi babban birnin kasar.

Dalilin hakan kuwa shine yadda harkokin rayuwar yau da kullun dake da nasaba da tattalin arzikin wannan kasa ya lalace.

Yau lahadi, ita ce ranar tunawa da cika shekaru 7 da aka samu wadannan tashe-tashen hankulan da ya haifar da zanga-zanga a kusan daukacin kasashen larabawa.

Wanda shine ma yayi dalilin kawo karshen mulkin shugaba Zine El-Abidine Ben Ali wanda a lokacin ya kwashe shekaru 23 kan karagar mulki.

Aikin yi,Yanci da Martaban dana dama sune taken zanga-zangar da akayi awancan lokacin ko a yau ma sune aka sake dawo dasu.

Sai dai wata ‘yar kasar mai suna Fatma Ben Hassine tace wannan juyin juya Hali bai kawo musu ko wane irin canji.

Tace maimako ma al’amurra sai kara sukurkucewa suka yi,tace dama ita dai fatar ta shine ace an samu walwalar al’amurra.

Yau lahadi ne gwamnatin kasar ta bayyana cewa zata Kara kudin agaji na iyali da kashi kusan sama da dala 70.

Duk da ‘yan kasan sun kwashe kwanaki 7 suna zanga-zanga kan shirin tsuke bakin aljihu da kasar ta kaddamar

Facebook Forum

Bidiyo

Yadda Wani Mutum Ya Mari Shugaban Faransa Emmanuel Macron
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:37 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Yadda Aka Yi Na Samu Mabiya Miliyan Daya a Shafina Na Instagram - Daso
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:34 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG