Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyoyi Masu Zaman Kansu A Bauchi Na ci Gaba Da Tallafawa Masu Zaman Kashe Wando


Kungiyar LIKEMINDS Mai Tallafawa 'Yan Gudun Hijira

A kokarin magance zaman kashe wando kungiyoyi masu zaman kansu suna koya wa mata da matasa aikin yi a jihar Bauchi.Kungiyoyin sunce suna samun nasarar wannan aikin ne domin suna samun tallafi daga hukumomin kasa da kasa irin su UNICEF.

Wata cibiyar tallafawa mata da matasa dake garin Bauchi mai suna “Rahama Women Development” ta dukufa wajen agaza wa mata da yara matasa domin samun abin yi.

Wasu daga cikin ayyukan da kungiyar ke koyarwa sun hada da yin man shafawa, sabulu, man gyaran gashi, da dai sauran abubuwan da ake anfani dasu cikin gida.

Malama Maryam Ilya ita ce shugabar wannan cibiyar kuma ta shaida wa wakilinmu Abdulwahab Mohammed cewa daga lokacin da kungiyar ta fara aiki kawo yanzu an yaye dalibai sama da 400.

Tace manya-manyan kungiyoyi da hukumomin kasa da kasa na cikin jerin wadanda suke basu tallafi, ciki ko har da hukumar UNICEF.

Wasu daga cikin abubuwan da suka samu sun hada da kekunan dinki da yadudduka.

Ga Abdulwahab Mohammed da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:38 0:00

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG