Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyoyi Masu Zaman Kansu Sun Shiga Yaki Da Zazzabin Cizon Sauro


Sauro

Kungiyoyi masu zaman kansu sun fara gudummuwa a kokarin yaki da zazzabin cizon sauro a kauyukan da ke kewayen babban birnin tarayya Abuja.

Kungiyoyi masu zaman kansu sun fara gudummuwa a kokarin yaki da zazzabin cizon sauro a kauyukan da ke kewayen babban birnin tarayya Abuja.

Kungiyoyin suna bada gudummuwa ta fannono dabam dabam da suka hada da gwaji domin tantance masu dauke da kwayar cutar.

Sakamakon gwajin magani da akayi bada dadewa ba a kan mazaunar garin zaki biyu a kauyen Jabi dake birnin tarayya Abuja ya nuna cewa mutane 40 a cikin 100 musamman yara, suna fama da zazzabin cizon sauro saboda yanayin garin.

Wata kungiya mai zaman kanta, Silver Lining for the Needy Initiative, ta dauki nauyin wannan gwajin. Binciken kungiyar ya nuna cewa, mutanen kauyen suna kuma zama a cikin wani yanayi na rashin tsabta da rashin cibiyoyin kula da lafiyarsu.

Bisa ga bayyanin kungiyar, shara da datti ya toshe magudanun ruwa abinda yake hana ruwa gudu ya kuma zama wurin tara sauro. Banda taimakawa wajen bincike masu dauke da cutar, kungiyar ta kuma taimaka wajen tsabtace muhallin da share magudanun ruwa, ta kuma bayyanawa mazauna kauyukan muhimmancin tsabtace muhallinsu musamman ganin ba a bari ruwa ya taru a wuraren da zai tara sauro ba.

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG