Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nijar-Kungiyoyin Fafutika Za Su Yi Zanga-zanga Kan Dokar Kara Haraji Ta 2018


Nouhou Arzik da sauran shugabannin kungiyoyin dake fafutika akan dokar haraji ta 2018

A jamhuriyar Niger shuwagabanin kungiyoyin farar hula sun bayyana shirin gudanar da zanga zanga a ranar 9 ga watan Satumban dake tafe da nufin sake jaddadawa mahukuntan kasar rashin amincewa su da dokar harajin 2018. Saboda rashin adalci ga talakawa.

Lura da yadda jama’a ke ci gaba da kokawa akan yanayin tsadar rayuwar da ake ciki a Nijer tun bayan kaddamar da dokar harajin 2018, ya sa wadanan kungiyoyin fararen hula a karksahin jagoracin Nouhou Arzika da Ali Idrissa da Moussa Tchangari, kiran daukacin ‘yan Niger su fito kan tituna a ranar 9 ga watan gobe a ci gaba da nuna adawa da wannan dokar haraji kamar yadda sanarwar da suka fitar ta fada.

Watanni sama da 8 kenan da hukumomin suka fara zartar da sabuwar dokar harajin da ake takaddama a kanta saboda haka Alhaji Usumana Mahamdu wani na kusa a jam’iyar PNDS mai mulkin kasar, ke ganin masu fafutika sun makara. A cewarsa 'ya Niger yanzu sun gane cewa masu fafutikan ba domin talakawa suke yi ba, su na da wata manufar siyasa.

Rufe ido akan dokar harajin 2018 tamkar sakarwa mahukuntar ragama ne su cusa wasu matakai na daban a daftarin dokar harajin shekara mai zuwa abin da ka iya kara jefa talakkawa cikin kuncin rayuwa inji Nouhou Arzika.

Tun a karshen shekarar 2017 ne kungiyoyin fafutika suka kaddamar da gwagwarmaya domin tilastawa gwamnatin kasar ta canza ra’ayi akan wasu sabbin matakan da ke kunshe a dokar harajin 2018. Sai dai kawo yanzu haka ba ta cimma ruwa ba, hasalima jagororin wannan tafiya sun tsinci kansu a gidan yari saboda zargin tada zaune tsaye, kafin a karshen watan jiya kotun Yamai ta sakesu.

A saurari rahoton Souley Barma

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:46 0:00

Facebook Forum

Shugaban Azman

Dalilin Da Yasa Muka Dakatar Da Tafiya Yajin Aikin Sufurin Jiragen Sama a Najeriya - Shugaban Azman
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:17 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Sojojin Najeriya sun samu nasarar kwace bindigogi sama da 500

Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Shugaban NDLEA a Najeriya, Janar Buba Marwa

Dalilin Da Ya Sa Muke Bin Diddigin Dukiyar DCP Abba Kyari - Buba Marwa
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:34 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Yadda Rikicin ‘Yan Aware A Yankin Kamaru Ya Shafi Wasu Al’ummoni A Najeriya

Yadda Rikicin ‘Yan Aware A Yankin Kamaru Ya Shafi Wasu Al’ummoni A Najeriya
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:19 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Gwamna Matawalle

Dalilan Da Suka Sa Muka Sayi Motoci Ga Sarakuna A Zamfara - Gwamna Matawalle
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:35 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG