Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyoyin Farar Hula Sun Lashi Takobin Mayarda Martani Kan Gangamin Goyon Bayan Shugaban Kasar Nijar


Seni Oumarou dan adawa wanda jam'iyyarsa ta shiga gwamnati da Issoufou Mahamadou, shugaban kasar Nijar

Yaynda jam'iyyun dake mulki a Nijar suka shirya gangamin goyon bayan shugaban kasa Issoufou Mahamadou jiya, kungiyoyin farar hula da suka yi zanga zanga bara domin jawo hankalin gwamnatin kasar aka kuncin rayuwa da talakawa ke ciki sun lashi takobin mayarda martani da fitowa wani sabon gangamin cikin wannan watan

Inji mai magana da yawun hadakar kungiyoyin farar hula na kasar Nijar Musa Cangari 'yan siyasa masu adawa da 'yan siyasa masu mulki duk tafiyarsu daya domin suna da alaka da juna.

'Yan adawa ne suka taimakawa jam'iyyar dake mulki yanzu har ta dare kan karagar shugabancin kasar. Yace masu mulki ba sa son su ji akwai matsala a kasar Nija domin basu san yadda zasu fito masu ba. Yace watakila kasawa ce.

Kungiyoyin ne suka shirya zanga zangar 21 ga watan Disambar bara saboda kokarin da suka yi na jawo hankalin gwamnatin kasar akan kuncin rayuwar talakawa. A wannan karon ma sun jaddada sake shirya wata zanga zangar a matsayin maidawa gwamnati martani.

Zasu yi zanga zangar ranar 13 ga wannan watan domin matsawa shugaban kasar Issoufou Mahamadou lamba ya hanzarta biya masu bukata da kuma mayarda martani bisa gangamin goyon bayan shugaban da aka gudanar jiya, inji Musa Cangari shugaban hadakar kungiyoyin.

Ga rahoton Souley Barma da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:36 0:00
Shiga Kai Tsaye

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG