Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyoyin Mata A Sudan Ta Kudu Na Bukatar A Dama Dasu


Kungiyoyin mata masu rajin ganin mata sun shiga an dama dasu, a gwamnatin kasar Sudan ta Kudu sunyi wani babban yunkuri.

Shuwagabannin mata na kasar Sudan ta Kudu, sun bukaci shugaban kasar da ya baiwa mata kashi 35 daga cikin dari kamar yadda yarjejeniyar samun zaman lafiya a kasar ta tanada.

Ranar Talata shugaban kasar Salva Kiir, ya nada kwamiti mai mutane 10 da aka dorawa nauyin fara shirin kafa gwamnatin wucin gadi. Mace daya kurum ya nada cikin kwamitin mai mutane 10.

Mary Ayen Majok, mamba a kwamitin ta bayyana ma VOA jiya Laraba cewar, ba suji dadin gwamnatin, bata baiwa mata kason da yarjejeniyar ta tanada ba.

Ba’a kaddamar da wannan shirin na baiwa mata kashi 35 cikin 100 ba a cewar Majok. Gare mu kuwa bamu ji dadin hakan ba, don hakan na nufin bangarorin basu mutunta ka’idodin yarjejeniyar da aka cimma a Addis Ababa ba.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG