Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyoyin yan yakin sa kai a Nigeria sun mika makamansu


Wasu bukkoki a yankin Niger Delta dab da gaba

Wasu kungiyoyin yan yakin sa kai a yankin Niger Delta mai arzikin mai na Nigeria, wadanda a baya suka yi kunnen kashi ga tayin ahuwa, yanzu suna mika makamansu.

A kwanan nan wasu kungiyoyin yan yakin sa kai na yankin Niger Delta mai arzikin mai na Nigeria, wadanda ada suka yi biris da tayin ahuwa da gwamnati tayi musu, yanzu suna tururuwar mika makamansu.

Kodayake wa'adin yin ahuwan yan kare, duk da haka gwamnati tayi maraba da wannan mataki. Kwamishinan yan sandan jihar Bayelsa Alhaji Aliyu Musa ya baiyanawa sashen Hausa na Muryar Amirka yadda yan yakin sa kan suke ci gaba da mika makamansu. Kwamishian yace duk wanda aka kama yana okarin tada zaune tsaye, to ya kuka da kansa.

XS
SM
MD
LG