Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kura Ta Lafa Bayan Fashewar Bam a Birnin Aba, Jihar Abia


 Kwamishanan 'yan sandan jihar Abia
Kwamishanan 'yan sandan jihar Abia

Bayan fashewar bam a Birnin Aban jihar Abia ranar Asabar da ta gabata, yanzu kura ta lafa domin baza jami’an tsaro da aka yi, mutane kuma na ci gaba da harkokinsu kamar yadda suka saba

Bayanai daga Birnin Aba dake jihar Abia na cewa komi ya lafa bayan fashewar wani bam ranar Asabar da ta gabata wanda ya raunata mutane amma bai kashe kowa ba.

Wasu mazauna Birnin sun shidawa Muryar Amurka jiya Lahadi abun da ya faru.

Alhaji Muhammad Tukura y ace wasu ne suka zo bayan an yi sallar isha’i suka tada bam da ya jikata mutane shida. An sallami hudu daga asibiti sauran biyun kuma suna nan kwance. Yau Litinin za’a yi masu tiyata a cire harsashan dake jikinsu.

An baza sojoji a Birnin domin tabbatar da tsaro kuma kawo yanzu hakan ya tabbata.

Shi ko Malam Garba Talley a yi amanna da bayanin Alhaji Tukura ind y ace sunfito salla ke nan sai wasu ‘yan iska suka tada bam. Allah ya takaita babu mutuwa sai dai rauni da mutane suka ji. Y ace mutane uku ne suka zo cikin keke napep tare da mace daya. Jami’an tsaro sun cafke daya daga cikinsu.

To sai dai kwamishanan yada labaran jihar Chief John Kalu ya musanta fashewar bam din saboda wai shi da gwamnan suna Birnin Aban bas u ji labarin fashewar komi ba.

Ga rahoton Alphonsus Okoroigwe da karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:57 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG