Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kwamandan Kungiyar Al-Shabab Yayi Saranda Ga Sojojin Somaliya


Shabaab

Hukumomin kasar Somaliya sunce wani kwamandan kungiyar yan tawayen Somaliya ta Al Shabab mai suna Bishar Mumin Farah, jiya Laraba yayi saranda ga sojojin gwamnatin kasar.

Ministan yada labaru na kasar Abdirahaman Omar Osman ya tabbatar kwamandan na Al Shabab Bishar Mumin Farah yayi saranda jiya Laraba a yankin Hiran dake kudu maso tsakiyar kasar

Wani jami’in sojan Somaliya mai mukamin Janaral da ya yiwa kwamandan Al Shabab tambayoyi ya fadawa Muryar Amirka cewa kungyar Al Shabab ta tura kwamandan zuwa Hiran wani baban yakin kasar Somaliya wanda ke da kimamin mutane miliyan guda, yawancinsu manoma, domin ya kai musu hare hare kuma ya kashe su cikin wannan wata na azumi.

Kwamandan na Al Shabab yayi saranda kuma ya mikawa sojoji bindigogi masu sarrafa kansu samfurin AK 47.

Facebook Forum

Matsalar Tsaro A Zamfara

Ko Kun San Irin Makaman Da Sojoji Ke Amfani Da Su Wajen Yaki Da 'Yan Bindiga A Jihar Zamfara?
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:31 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Kamu A Auren Nupawa

Yadda Nupawa Suke Kamun Ango A Bikin Aure
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:21 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG