Yayin da ya rage makoni a gudanar da zabubbuka a Najeriya, Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Borno, Clement Aduda, ya gargadi ‘yan siyasa dasu guji amfani da kalamai na batanci, domin kaucewa fitina.
Kwamishinan ya bayana hakan ne a lokacin da yake ganawa da ‘yan siyasa, a hedkwatan ‘yan sandan jihar a Maiduguri.
Ya kara da cewa irin wannan rigingimu da rashin zaman lafiya dake fuskantar alumar jihar, ka dai abun damuwane, bai kuma kyautu wani dan siyasa ya tada hankalin ko kuma amfani da kalmomin batancin ga wani dan siyasa ba.
A yanzu haka dai jihar Borno, masamman babban birnin Maiduguri, na ci gaba da tunbatsa ne da ‘yan gudun hijira, a daidai lokacin da ‘yan Boko Haram, ke ci gaba da mamaye wasu kananan hukumomi, dama karbe wasu barikokin sojoji.