Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sabon Kwamishinan 'Yansanda na Jihar Anambara ya Nemi Hadin Kai Daga Jama'ar Jihar


Wasu 'yan sandan Nijeriya a bakin aiki
Wasu 'yan sandan Nijeriya a bakin aiki

A hirasa ta farko da wakilin Sashen Hausa na Muriyar Amurka, Kwamishina Akilla Usman Gwari, yace wajibi ne jama'a su baiwa 'Yansanda hadin kai, kuddin ana son samun nasarar inganta harkokin tsaro.

Sabon kwamishinan 'Yansanda na jihar Anambra Akila Usman Gwari ya nemi hadin kai daga jama'ar jihar Anambra ta wajen baiwa rundunarsa bayanan sirri dangane da take- take, ko ayyukan mutane da suka sani cewa bata gari ne.

A hira da wakilin Sashen Hausa na Muriyar a Amurka a yankin, kwamishina Gwari yace saboda haka ne ma ya bada lambar woyarsa ga duk wanda yake da bayani da yake so ya baiwa hukumar ba tareda ya bayyana kansa ba. Mallam Akila yace mutane sun san wadanda suke tareda su saboda haka wajibi ne su bada gudumawarsu wajen ganin an inganta harkokin tsaro.

Da ya nemi jin ta bakin wasu daga cikin jama'ar jihar kan wannan kira da kwamishina Akila yayi, wakilin Sashen Hausa lamido Abubakar Sokoto yace wadanda ya zanta da su sun bayyana amincewarsu da tareda alkawarin bata hadin kai ga rundunar.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:13 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG