Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kwamitin Binciken Sakataren Gwamnati da Shugaban Hukumar NIA Ya Gama Bincikensa


Mukaddashin Shugaban Kasa Farfasa Yemi Osinbajo wanda ya jagoranci kwamitin binciken
Mukaddashin Shugaban Kasa Farfasa Yemi Osinbajo wanda ya jagoranci kwamitin binciken

Bincike ya nuna kwamitin da shugaba Buhari ya kafa domin ya binciki zargin da ake yiwa Sakataren gwamnati David Babachir Lawan da yake fuskantar zargin yin zarmiya da shugaban hukumar leken asirin kasashen waje NIA, Yemi Oke, ya kammala aikinsa gap da lokacin da shugaban kasa zai koma Ingila wajen jinya

Mika rahoton ya zo daidai da lokacin da Shugaba Muhammad Buhari yake shirin komawa Ingila ganin likitocinsa.

Dole yanzu kwamitin ya jira umurnin shugaban kasa ko dawowarsa kafin a bayyana sakamakon binciken da matakan da gwamnati zata dauka. Mukaddashin ba zai bayyana matakin gwamnatin ba domin shi ne ya jagoranci binciken.

Ministan Shari'a Abubakar Malami da mai bada shawara akan harkokin tsaro Janar Babagana Mongunu suna cikin kwamitin binciken.

A cewar Abubakar Malami tunda Farfasa Osinbajo ne ya jagoranci kwamitin ba zai riga malam masallaci ba. Hakkin mataimakin shugaban kasa ne ya yiwa shugaban kasa bayani akan bincikensu. Saboda haka shugaban kasa ne kadai zai iya yin bayani tare da irin matakan da zai dauka.

Kakakin shugaban kasa ya bada tabbacin yin adalci dangane da sakamakon binciken. Yace idan kuma majalisa tayi nata ta kawo shugaban kasa zai duba kuma zai tabbatar an kare abun da ya shafi kasa da bin doka da ka'ida.

Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:49 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG