Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kakakin Majalisar Dokokin Ghana Ya Kafa Kwamitin Cin Hanci Da Rashawa


A yau ne wani kwamiti na musamma da kakakin majalisa dokoki a Ghana Prof. Mike Oquaye ya kafa domin ya bincike zargin bayarwa da karbar rashawa a majalisar karkashin wani babban lauya mai suna Joe Ghartey, zai fara aiki inda zai bi diddigin batun zargin da ake yiwa ministan makamashi Mr Boakyei Agyarko.

Dan majalisa a mazabar Bawku Central, yana zargin ministan Makamashin da basu cin hancin sidi dubu uku uku ta hannun mai tsawatarwa na bangaren marasa rinjayi Muntaka Mohammed don su yi masa sassauci a wurin tantance shi.

Tuni dai Muntaka Mohammed ya musunta wannan zargi da akace anyi amfani da shi wurin bada cin hancin a cewar Mahama Ayariga da wasu abokan aikinsa.

Wasu wakilan majalisar dokokin na bangaren marasa rinjayin da suka hada da Okudzeto Ablakwa da Alhaji Alhassan Suyini sun fito karara suka tabbatar da su kuma sun samu wani kudin.

Mr. Boakye Agyarko da ake zarginsa da bada cin hanci shi kuma ya musunta wannan zargi kuma ya yi barazanan daukar mataki a huskar doka.

Duk da musuntawa da Boakye Agyarko da aka ce ya bada kudin da Muntaka Mohammed da ya karbi kudin ya kaiwa mutanensa marasa rinjayi, Mahaman Ayariga tare da Okudzeto Ablakwa da Alhassan Suyini sun yi tsayin daka a bakansu cewa lallai an bada cin hanci don jan ra’ayinsu kuma sun yi kira da kakakin majalisar ya kafa bincike a kan lamarin.

Komiti na musamman da kakakin majalisar ya kafa karkashin shugaban shi Joe Ghartey, yana da mambobi kamar Ben Abdallah wakilin mazabar Ofinso, da Ama Pomaa Boateng daga mazabar Juabeng, daBT Baba mazabar Talensi da kuma Magnus Kofi Amoateng.

XS
SM
MD
LG