Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kwamitin Da'a Na Majalisar Dattawa Bai Gayyaci Kwastan Akan Motar Da Ta Kama Ba


Hedkwatar Hukumar Kwastan dake Abuja
Hedkwatar Hukumar Kwastan dake Abuja

Mai magana da yawun hukumar kwastan ya gayawa Muryar Amurka cewa ba'a gayyaci hukumar ba su ma sun ganin sun kuma ji ta kafar talibijan ne suka ji zaman kwamitin da'a na Majalisar Dattawa akan motar da suka kama.

Inji kakakin hukumar kwastan ashirye suke su bayyana a gaban kwamitin da'a na majalisar dattawa suyi bayani dalla dalla akan motar da suka kama .

Jami'in labarun hukumar kwastan din Joseph Atta ya musanta dalilin da ya sa shugaban hukumar bai bayyana gaban kwamitin ba don yin bayani akan motar. Hamid Ali bai ki bayyana ba saboda takaddamar dake tsakaninshi da Majalisar akan sanya kayan sarki.

Ita motar dai tun watan Janairu hukumar kwastan ta kamata a Legas saboda wai Sanata Bukola Saraki da aka ce motar tashi ce bai biya harajin Naira miliyan saba'in da hudu ba.

To saidai lokacin da shugaban Majalisar Dattawan Dr Bukola Saraki ya bayyana a gaban kwamitin ya musanta shigo da motar yana mai cewa Majalisar ce ta sayeta. Yace yawancin motocin majalisar ba za'a san an yi odarsu ba sai an kawosu. Ya nuna motar mallakar Majalisar Dattawa ce.

Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:18 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG