Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kwamitin Sulhu Na MDD Ya Sabunta Kudurin Zaman Lafiya A Sudan ta Kudu


Taron Kwamitin Sulhu na MDD akan Sudan ta Kudu

Majalisar Dinkin Duniya ta sake sabunta kudurin zaman lafiya a Sudan ta Kudu tare da yin barazanar ladaftar da duk wanda ya hana ruwa gudu a shirin zaman lafiyar kasar kamar yadda ya faru a can baya

Kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, MDD, a jiya Alhamis ya sake sabunta kudirin sa na samar da zanman lafiya a Sudan ta Kudu har na wani tsawon shekara gudatare da barazanan sawa kasar takunkumi game da makamai muddin dai aka ci gaba da fada.

Kudirin wanda Amurka ce ta aike dashi wajen taron ta bayyana cewakwamitin na duba yiwuwar daukar dukkan matakan da suka dace akan duk wasu masu kokarin kawo wa zaman lafiya da tsaro cikas a kasar ta Sudan ta Kudu.

Tace tana ganin dakatar da sayar da makamai da shiga dasu cikin kasar zai durkusad da sassan biyu masu fada da juna.

A cikin shekarar 2011 ne Kasar ta Sudan ta Kudu ta samu yancin ta daga Kasar Sudan, amma kuma tun daga wannan lokacin yakin basasa ya barke tsakanin sassa biyu, wato tsakanin bangaren shugaban kasa Salva Kiir da mataimakin shugaban kasa Riek Machar.

Ko a cikin watan disamban bara an sa hannu akan samar da zaman lafiya amma hakan bai yi nasara ba.

Yanzu haka dai kasar tana fama da matsanancin rashin abinci, domin an kiyasta cewa mutane da suka kai miliyan 4 sun bar kasar da yaki, talauci, don tsananin yunwa data addabe su

Wannan yasa kasar ta zama kasar dake kan gaba a duk fadin duniya da yan gudun hijiran suka fi kowa zama cikin matsanancin damuwa.

Wani kwararre a harkan kare hakkin bil adama na MDD yace a kalla jami’an gwamnatin kasar da sojoji sama da 40 ne yanzu haka suke fuskantar tuhuma akan aikata ba dai-dai ba ga al’umma.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG