Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kwamitin sulhu yace zai azawa bangarorin Sudan ta kudu takunkumi


Shugaban Sudan ta kudu Salva Kir a Juba

Kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya yace a shirye yake ya azawa bangarorin kasar Sudan ta kudu takunkumi, idan basu kaddamar da sabuwar yarjejeniyar samun zaman lafiya kacokan dinta ba.

Kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya yace a shirye yake ya azawa bangarorin kasar Sudan ta kudu takunkumi, idan basu kaddamar da sabuwar yarjejeniyar samun zaman lafiya kacokan dinta ba.

A wata sanarwar daya gabatar jiya Juma'a, wakilan kwamitin goma sha biyar sunyi kira ga dukkan bangarorin Sudan ta kudu da su mutunta ka'idodin yarjejeniyar nan take.
A ranar Alhamis shugaban Sudan ta kudu Salva Kir ya baiwa rundunar sojan kasar umarnin da su dakatar da dukkan hare haren da suke kaiwa. Ya bada wannan umarnin ne kafin a fara amfani da yarjejeniyar samun zaman lafiya a yau Asabar din nan cikin yardar Allah.
A ranar Laraba shugaba Salva Kir ya rattabawa yarjejeniyar hannu a Juba, mako guda bayan da shugaban yan tawayen Reik Machar ya rattabawa yarjejeniyar hannu a birnin Addis Ababa to amma a lokacin Mr Kir ya baiyana tababar sa akan yarjejeniyar, al'amarin daya sa aka yi da baiyana tsoron cewa kila yarjejeniya ba zata kankama ba
Wata sanarwar da Majalisar Dinkin Duniya ta gabatar ya nuna damuwa akan duk wata sanarwar da kowane bangare na Sudan ta kudu zai gabatar da zata nuna rashin aniyar kaddamar da yarjejeniyar.
Kula wannan yarjejeniya ta biyo bayan shawarwari da aka yi wata da watani ana yi a kasar Ethiopia da kuma karya alkawuran yarjeniyoyin baya da bangarorin Sudan ta kudu suka sha yi.

XS
SM
MD
LG