Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kwamitin Tsaro Na MDD Yace Adama Barrow Ne Ya Sani A Matsayin Shugaban Gambia


Adama Barrow sabon shugaban Gambia bayan da aka rantsar dashi

Kwamitin Tsaro na M-D-D yace daga yau, Adama Barrow ne kawai ya sani a matsayin shugaban kasar Gambia, duk da cewa har yanzu tsohon shugaban Yahya Jammeh na ci gaba da cewa shi ba zai sauka ba.

A jiya Alhamis ne aka rantsarda Adama Barrow a matsayin sabon shugaba a wani shagalin da aka gudanar a Opishin Jakadancin Gambia dake kasar Senegal. Kamata yayi ace a birnin Banjul aka rantsar da shi amma saboda yadda abubuwa suke, tilas aka chanja.

Wani hafsan sojan kasar ta Senegal ya gaya wa kampunnan watsa labaran Yammaccin Turai tun jiya cewa tuni sojan Senegal suka tsallaka zuwa cikin Gambia din, yayinda wani jam’in gwamnatin Nigeria ya tabattarda cewa su ma sojan Nigeria din suna cikin wannan yunkurin na tabattarda zaman lafiyar Gambia.

Izuwa yanzu dai ba wani rahoto dake nuna cewa ana wani tashin hankali a Gambia.

Kakakin Ma’aikatar harakokin Wajen Amurka John Kirby yace Amurka na goyon bayan wannan matakin anfani da karfin soja da kasashen Afrika ta Yamma suke dauka akan Gambia.

An Ga Watan Azumi A Najeriya - Sultan

Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammada Sa'ad Abubakar Ya Ba Da Sanrwar Ganin Watan Ramadan
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:21 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
Wani Sirri Da Tsohon Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou Ya Fadawa ‘Sarki Sanusi II’
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:23 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

An Kai Wa Ofisoshin Kungiyar Ba Da Agaji Hari A Arewa Maso Gabashin Najeriya
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:02 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG