Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kwamitin Tsugunar Da Wadanda Rikici Ya Shafa A Plato Ya Mika Rahoto

Kwamitin da gwamnan jahar Pilato Simon Lalong ya kafa domin maida ‘yan gudun hijirar jahar zuwa garuruwansu na asali ya mika rahoto.

Rahoton na nuni da cewa, fiye da mutane dubu hamsin da tara ne rikicin da ya auku a kananan hukumomi biyar na jahar ya shafa yayinda mutane dubu hamsin da dari biyu da goma sha biyu ke gudun hijira.

Kananan hukumomin da komitin yayi nazari a kansu sun hada da Jos ta Arewa, Bassa, Riyom, Barkin Ladi da Bokkos.

Domin Kari

16x9 Image

Grace Alheri Abdu

Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

XS
SM
MD
LG