Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kwanakin Julen a Real Madrid Na Kara Zama Kayyadaddu


Rahotanni na nuni da cewar Kungiyar Real Madrid da ke kasar Spain, tana tunanin sallamar kocinta Julen Lopetegui, mai shekaru 52, a Litinin din nan bayan da ya gaza samun nasara a wasannin da kungiyar ke bugawa.

Daga cikin wasannin har da babban wasan da suka yi da Barcelona na El-Classico a ranar Lahadi inda aka lallasa Real da ci 5-1.

Sai dai ana ganin tsohon kocin Chelsea Antony Conte, shi ne ya ke kan gaba wajan maye gurbin Lopetegui in har Real ta sallame shi duk da yana da sauran yarjejeniyar kwantiraginsa a kungiyar zuwa 2022.

A bangaren guda kuwa mataimakin shugaban Kungiyar kwallon kafa ta Juventus da ke kasar Italiya, Pavel Nedved, ya bayyana wa manema labarai cewa ko kadan babu wani batu kan rade-radin da ake yi na cewar za su dawo da tsohon dan wasan su Paul Pogba mai shekaru 25 da haihuwa zuwa kulob din daga Manchester United.

Manchester United ce ta sayar da Pogba ga Juventus a matsayin kyauta wato (Free Transfer) daga bisani ta sake dawowa ta saye shi da tsada, Inda a shekarar ya kasance dan wasan kwallon kafa mafi tsada a duniya a wannan shekarar.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:00 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG