Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kwanan Nan Kungiyar Boko Haram Za Ta Zama Tarihi Inji Buhari


Shugaba Muhammadu Buhari

A kokarinsa na kara karfin gwiwa ma 'yan gudun hijirar rikicin Boko Haram, Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce da yaddar Allah kashin 'yan Boko Haram zai bushe kwanan nan.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce an kusa ganin bayan Boko Haram da izinin Allah. Shugaba Buhari, wanda ya ziyarci sansanin ‘yan gudun hijira na Malkohi a jahar Adamawa ya yi wa mutanen da ‘yan Boko Haram su ka raba da muhallansu alkawarin cewa za su koma gidajensu ba da dadewa ba.

Shugaba Buhari ya bayyana ‘yan Boko Haram da marasa addini, wadanda sam ba su da Imani, sannan ya sake jaddada cewa kwanan nan za su zama tarihi. Y ace ‘yan Boko Haram na zuwa wuraren ibada sun a ta kashe mutane cikin rashin tausayawa da rashin Imani.

Shugaban na Najeriya ya yada zango a sansanin ‘yan gudun hijirar ne yayin da ya halarci bukin daurin auren 'ya'yan tsohon Mataimakin Najeriya kuma jigo a jam’iyyar APC mai mulki Alhaji Atiku Abubakar.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:19 0:00

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG