Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kwango Ta Ayyana Dokar-Ta-Bacin Polio A Fadin Kasar


Kwango Ta Ayyana Dokar-Ta-Bacin Polio A Fadin Kasar
Kwango Ta Ayyana Dokar-Ta-Bacin Polio A Fadin Kasar

Mutane 201 sun samu shanyewar jiki, mutane 104 kuma sun mutu a dalilin annobar cutar Polio da ta bulla a Kwango-Brazzaville

Mummunar annoba ta cutar shan inna, ko Polio, ta barke a Jamhuriyar Kwango (Kwango-Brazzaville), inda Hukumar Kiwon Lafiya ta Duniya ta ce a cikin makonni biyun da suka shige kadai, mutane 201 sun samu shanyewar jiki, mutane 104 kuma sun mutu.

Gwamnati a birnin Brazzaville ta ayyana dokar-ta-baci ta cutar Polio, ta kuma bayyana shirin bayar da maganin rigakafin cutar sau uku ga illahirin jama’ar kasar tare da taimakon Hukumar Kiwon Lafiya ta Duniya, da Asusn Yara na Majalisar Dinkin Duniya, da kuma Cibiyar Rigakafi da Yaki da Yaduwar Cututtuka ta kasar Amurka.

Darektan yaki da cutar Polio a duniya a Hukumar Kiwon lafiya ta Duniya, Dr. Bruce Aylward, ya ce a birnin Pointe Noire mai tashar jiragen ruwa, inda wannan cuta ta fi tsanani da yawa, “muna da daruruwan mutanen da jikinsu ya shanye, da matattu masu yawa a wasu asibitoci biyu” a birnin. Ya kara da cewa, “Akwai wasu abubuwa na dabam, masu tayar da hankali sosai a wannan sabuwar annobar (polio) da ta bulla a Kwango.”

Akasari, cutar Polio tana kama yara maza da mata daidai wa daida ne, kuma ba ta kashe fiye da kashi 20 cikin 100 na wadanda ta sa jikinsu ya shanye. Mutuwar tana zuwa idan shanyewar jiki ta bi ta cikin bargon gadon baya ta kai ga jijiyoyin aikewa da sakonni masu kula da yadda mutum yake numfashi. A wannan karon a birnin Pointe Noire, kashi 85 cikin 100 na wadanda suka kamu da cutar ta Polio matasa ne da balagaggu, akasarinsu maza, kuma yawan wadanda suke mutuwa ya zarce yadda aka saba gani nesa ba kusa ba.

Dr. Aylward yace tawagarsa tana kan hanyar zuwa Kwango domin bin diddigin wannan sabuwar annoba.

Kyamfe na yaki da Cutar Polio a Kasar Angola, 2010
Kyamfe na yaki da Cutar Polio a Kasar Angola, 2010

An fara bayar da magungunan rigakafin kamuwa da cuytar Polio a yankin tsakiyar Afirka a shekarun 1980, inda aka fi mayar da hankali a kan yara ‘yan kasa da shekara 5. Wannan na nufin cewa mutanen da suka balaga kadan suke da kariyar rigakafin. Haka kuma, kwayar cutar da aka kashe mata kaifi ake kuma bayar da ita a cikin ruwan maganin rigakafin, ita ma tana yaduwa kamar yadda cutar ta ainihi take yaduwa, watau ta cikin bayangida. Ma’ana, mata sun samu kariya daga cutar a fakaice a saboda uwaye da kuma yara mata a gida sune suke canja ma yara kanana wando idan sun yi kashi.

Dr. Aylward yace za a dauki makonni kafin a san ko gagarumin aikin rigakafin cutar Polio da aka kaddamar a yankin tsakiyar Afirka a cikin ‘yan shekarun baya zai iya shawo kan wannan annobar. Ya bayyana wannan lamari na Kwango a zaman koma-baya a wannan shekarar da aka samu ci gaba sosai a yaki da cutar Polio.

Alal misali a Najeriya, kasar da ta jima tana zaman tungar cutar Polio a nahiyar Afirka, ta samu raguwar wannan cuta da kashi 98 cikin 100 kama daga shekarar 2009 zuwa yanzu. Haka kuma, kasashe 14 daga cikin kasashe 15 da aka ga jinsin cutar Polio irinta Najeriya a cikinsu sun samu nasarar kawar da ita.

Jinsin kwayar cutar Polio dake kisa yanzu a Kwango-Brazzaville, ta kasar Indiya ce wadda aka fara gani a kasar Angola a shekarar 2007, wadda kuma a yanzu aka ce tana yaduwa arewa.

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG