Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kwararru Sun Bayyana Irin Shugaban Kasar Da Najeriya Ke Bukata


Rumfar kada kuri'a a Najeriya a Yola a zaben 2019.
Rumfar kada kuri'a a Najeriya a Yola a zaben 2019.

Ya zama mai muhimmanci ‘yan Najeriya su kawar da bambance-bambancen kabilanci, wariya don addini da yanki matukar kasar za ta tsira daga talauci, rashin tsaro da guguwar ‘yan a fasa kowa ma ya rasa.

Yayin da masu sha’awar takarar shugabancin Najeriya a badi ke kara bayyana muradinsu, tsohon shugaban zauren jam’iyyu Yunusa Tanko ya ce za a iya samun garambawul ga tsarin shugabancin Najeriya don biyan muradun talakawa ta hanyar zakulo ‘yan takara da ba su da bashin ramuwar wani abun da a ka yi mu su a baya.

Tanko na magana ne a taron da wasu sanannun ‘yan siyasa su ka kira don duba sabbin fuska da su ke ganin ya dace a gwada su a kan madafun iko a babban zaben mai zuwa.

Yunusa Tanko wanda ke jagorantar jam’iyyar NCP da marigayi lauya Gani Fawahinmi ya kafa, ya ce Najeriya na bukatar sabon salon siyasa don kaucewa yadda ya ce aka kawo Obasanjo a 1999 don wanke fusatar magoya bayan Abiola da aka soke zaben sa a 1993, kazalika ya kasance ya na kullace da marigayi Janar Abacha wanda ya tura shi gidan yari da tuhumar juyin mulki.

Duk da Tanko bai ambaci sunan shugaba Buhari ba, ya ce wadanda su ka dade su na jan ragamar Najeriya a soja da farar hula sun kure wa’adin damar su ta iya dawo da Najeriya kan turba.

A na sa bangare tsohon ministan matasa da wasanni Solomon Dalung ya yi wasu tambayoyi ne kan yadda yake ganin za a sha wuya wajen yi wa talakawa kamfen da alkawuran da a baya ba a samu cikawa ba.

Zuwa yanzu dai ba a tsira daga batun damar ‘yan arewa ko ta ‘yan kudu wajen amsar ragamar mulki ba maimakon a ce za a iya samun dan takara mai tsayawa don cancantarsa kadai.

“Ba bangaren shugaban kasa ba ne kadai ya gaza, ka je ka duba shugaban karamar hukumar ka, za ka taras ba zai rika zagawa ya na duba inda aka samu ramuka kan titi don a cike su ba, amma tunanin sa shi ne yadda za a samu kudi don bukukuwa ko raka gwamna taruka,” in ji Barista Adewole Adebayo daga jihar Ondo da ke cikin maso son takarar shugaban kasa a 2023”

Barista Adebayo ya ci gaba da cewa za ka ga ministoci na zuwa taron majalisar zartarwa duk Laraba don ba da kwangiloli amma ba mai iya tambayar inda a ka kwana a kwangilolin da a ka bayar a baya.

Ya zama mai muhimmanci ‘yan Najeriya su kawar da bambance-bambancen kabilanci, wariya don addini da yanki matukar kasar za ta tsira daga talauci, rashin tsaro da guguwar ‘yan a fasa kowa ma ya rasa.

Zuwa yanzu dai a na sa ran gudanar da babban zaben a ranar 23 ga watan Febrairun badi tun da alamu na nuna an daidaita kan sabuwar dokar zabe tsakanin shugaba Buhari da majalisar dokoki.

XS
SM
MD
LG