Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kwararru Sunce Ba Za A Sami Farfadowar Tattalin Arziki Sosai Ba Bana


Shugabar Asusun IMF Christine Lagarde
Kwararru a asusun bada lamuni na kasa da kasa sun ce farfadowar tattalin arzikin kasashen duniya zai rika tafiyar hawainiya bana, yayinda yiwuwar tsunduma cikin wadansu matsalolin tattalin arziki masu girma ke karuwa.

Asusun lamunin ya rage makin harsashen ci gaban tattalin arzikin kasashen duniya da ya yi, tun farko zuwa kashi uku da digo uku bisa dari.

Wannan harsashen ya sa hannayen jari da dama yin kasa a lokacin hada hadar hannayen jari jiya Talata.

Wannan na faruwa ne a daidai lokacin da manyan jami’an harkokin tattalin arziki na kasashen duniya suke taruwa a birnin Tokyo, domin halartar wani taron hukumar bada lamunin da kuma babban bankin duniya wannan makon.

Babban jami’I mai kwarewa kan tattalin arziki na cibiyar IMF Olivier Blanchard tace tafiyar hawainiyar da farfadowar tattalin arzikin kasashen da suka ci gaba ke yi, yana tauye ci gaban kasashe masu tasowa.

Bilanchard ya yi gargadi da cewa, lamura zasu kara rincabewa idan Washington da kuma kasashen Turai suka gaza shawo kan matsalolinsu na siyasa da kuma kudi take yanke.
XS
SM
MD
LG