Wannan binciken ya kara taimakawa wajen samar da karin magani domin shawo kan yaduwar cutar, ta wurin kashe kwayar cutar da ke cikin jini.
Koda yake masu binciken sun sani shekaru da dama da suka wuce cewa, jinin da ya hadu da kwayar malariya, zai iya kashe wanda yake dauke da cutar, yanzu an gane hanyoyin kauda wannan malariya mai babbar matsala. Yanzu a wani bincike da aka yi a jaridar Nature, masu binciken sun gano cewa wannan tana kama kayan cikin jini, wadda ke hana kamewar jini.
Tana kuma kawo cutar kwakwalwa. A shekara ta 2012, kungiyar masu bincike uku sun gano cewa akwai wani irin PfEMP1 protein shine ke kawo cutar kwakwalwa daban. Duk da haka, har yanzu, ba’a gano abinda ke ajiye ta ba, wata tambayar itace, wane jini kwayar take kamawa.