Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Lady Gaga, Jennifer Lopez Sun Cashe a Bikin Rantsar Da Biden


Jennifer Lopez, hagu da Lady Gaga, dama

Shahararrun mawaka Lady Gaga da Jennifer Lopez na daga cikin mawakan da suka cashe a bikin rantsar da shugaban Amurka Joe Biden a ranar Laraba 20 ga watan Janairu.

Ita dai Gaga ta kasance daya daga cikin masu marawa Biden baya, inda akan ganta ta na bin gangamin yakin neman zabensa gabanin zaben watan Nuwambar bara.

Kwamitin da ya tsara bikin rantsar da Biden ne gayyaci Gaga inda ta rera taken kasar a ranar 20 ga watan Janairu, 2021.

Hakan ya sa Gaga ta yi maza ta shiga shafinta na Twitter, don nuna godiyarta da wannan karramawa da aka mata.

“Na yi matukar jin dadin wannan karramawa da aka min na shiga @BidenInaugural bikin rantsar da Biden a ranar 20 ga watan Janairu don na rera taken kasa a wannan biki mai dumbin tarihi na @joebiden da @kamalaharis!” Gaga ta rubuta a shafinta na Twitter.

Baya ga Gaga, wata mawakiya da aka gayyata ita ce J-Lo wacce ita ma ta bibiyi gangamin yakin neman zaben Biden gab da yin zabe.

Bidiyo

Saurari Dalilin Da Ya Sa Ummi Zeezee Ta Ce Tana So Ta Kashe Kanta A Hira Da Wakiliyar VOA Baraka Bashir
please wait

No media source currently available

0:00 0:06:39 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

VOA CASU

VOA CASU: Saurari Bayanin Jarumar Kannywood, Nafeesa Abdullahi
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:24 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

VOA CASU

VOA CASU: Bikin Yini Na Auren Zawarawa A Kano
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG