Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Lamidon Adamawa Yayi Tsokaci Akan Zaman Lafiya Tsakanin Makiyaya da Manoma


Lamidon Adamawa Dr Mustapha Barkindo yana karbar gaisuwar sallah
Lamidon Adamawa Dr Mustapha Barkindo yana karbar gaisuwar sallah

Kamar yadda al'ada Ta tanada jama'a na kwararawa fadar Lamidon Adamawa Dr Barkindo Aliyu Mustapha domin mika gaisuwar sallah gareshi.

Duk da kokawa da halin kuncin rayuwa, jama'a a jihar Adamawa basu fasa yin abun da suke yi ba lokacin bikin sallah na zuwa gaida sarakuna.

Har yau ana cigaba da bukukuwan sallah inda mutane na tururuwa zuwa gaida manyan sarakuna.

Bikin gaida Lamidon Adamawa a fadarsa
Bikin gaida Lamidon Adamawa a fadarsa

A jawabinsa ga dimbim jama'a da suka taru a fadarsa, Lamidon Adamawa Dr. Barkindo Aliyu Mustapha kuma shugaban majalisar sarakunan jihar Adamawa yayi tsokaci ne dangane da samun zaman lafiya musamman tsakanin makiyaya da manoma.

Lamidon ya lura da irin mugun tashin hankalin dake faruwa tsakaninsu cikin 'yan kwanakin nan. Yace kullum yana samun rahotannin hasarar dukiyoyi da rayuka saboda rashin kauna, rashin imani da rashin fahimtar juna. Akwai kuma rashin kiyayewa da hakkin dake rataye kan kowa.

Sarkin ya kira jama'a da su hada kai tare da kiran gwamnati ta inganta tsaro da bada goyon baya iya gwargwado domin daukan matakan da suka dace.

Ya nuna farin cikinsa ga gwamnatin Adamawa saboda kebe kadada dubu biyar domin anfanin makiyaya, inda zasu dinga kiwo maimakon shiga gonakan mutane da dabbobinsu.

Ga rahoton Ibrahim Abdulazi da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:12 0:00

XS
SM
MD
LG