Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Lauyan Budurwar Stephen Paddock Wanda Ya Kashe Mutane a Las Vegas Yace Bata da Masaniya


Marilou Danley. Danley, 62, ita ce budurwar Stephen Paddock wanda ya kashe mutane da dama a Las Vegas

A cewar lauyan Marilou Danley mai shekaru 62 da haihuwa, budurwar Stephen Paddock wanda ya kashe mutane da dama a Las Vegas, bata da masaniya kan ayyukan ta'addancin da ya aikata

Lauyan budurwar ‘dan bindigar da ya kashe mutane a birnin Las Vegas na nan Amurka, Stephen Paddock, ya ce matar bata da masaniyar cewa Paddock yana kitsa aikata ta’addanci.

Budurwar ‘dan bindigar mai suna Marilou Danley, ta kwashe tsawon ranar jiya Laraba tana amsa tambayoyin jami’in hukumar binciken manyan laifuka ta Amurka FBI, a birnin Los Angeles, bayanda ta dawo Amurka daga tafiyar da tayi kasar Philippines.

Lauyan Danley ya fadawa manema labarai cewa ta yi bulaguro zuwa Philippines ne domin ta ziyarci danginta dake can kuma yayinda take a can din ne Paddock ya aika mata da zunzurutun kudi har Dalar Amurka Dubu 100, yace mata ta sayi gida.

Yayin da masu bincike ke kokarin gano dalilin da yasa Paddock ya kai harin ya kashe mutane 58 da raunata wasu sama da 500, shugaban kasar Amurka Donal Trump, ya kai ziyara a birnin na Las Vegas, don jajantawa wadanda lamarin ya shafa da kuma ganawa da ‘yan sanda da ma’aikatan agajin gaggawan da suka kai agajin farko.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG