Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Lauyan 'Yan Boko Haram da Ake Tuhuma Ya Zargi Babbar Kotun Tarayya da Son Rai


Wasu 'yan Boko Haram

Lauyan 'yan Boko Haram da ake tuhuma ya zargi babbar kotun tarayya da son kai lamarin da yace ya kawo shakka kan ko zasu samu hukunci mai adalci saboda haka alkalin kotun ya mayarwa alkalin alkalan kasar ya zabi wani alkalin

Lauyan ‘yan Boko Haram da ake tuhuma ya zargi babbar kotun tarayya da nuna son rai bias ga yadda ake tsare da ‘yan Boko Haram din a Hukumar DSS maimakon a gidan kaso.

Lauyan na shakkar ‘yan Boko Haram din ko zasu samu hukunci mai adalci.

Saidai a zantawa da yayi da manema labarai, lauyoyin gwamnati na cewa sun shirya tsaf su cigaba da shari’ar.

A wani yunkuri na daban, mai shari’a John Tsoho ya yanke hukuncin cigaba da yin shari’ar. Yanzu za’a mayar da batun babban kotun tarayya domin a mikawa wani alkalin shari’ar.

Barrister Ibrahim Tukur El-Sudi, lauyan tsarin mulki, yace ‘yan Boko Haram basu yarda da kotun kasar ba saboda haka zasu cigaba da yin korafe korafe har a gaji a yi watsi da korafin nasu.

Wani lauyan ma cewa yayi ‘yan Boko Haram din sun wuce gona da iri saboda wasu dalilai da ya lissafa.

Ga rahoton Hassan Maina Kaina da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:55 0:00

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG