Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

LEGAS: Gwamnati Ta Ba Masu Sana'ar Achaba Wa'adi Su Daidaita Sahunsu


Irin cinkoson Legas

Sakataren gwamnatin jihar Legas ya fitar da wata sanarwar ba masu sana'ar achaba da su daidaita sahunsu nan da kwanaki ashirin da daya ko kuma su fuskanci hushin gwamnatin

Mr. Tunji Bello sakataren gwamnatin Legas yace bincike ya nuna cewa 'yan achaba basu daina bin manyan tituna jihar ba kamar yadda aka umurcesu. Saboda hak an basu wa'adin kwanaki ashirin da daya su daina ko kuma su fuskanci hukunci.

To saidai masu sana'ar sun kira taron manema labarai sun bayyana gwamnatin ta Legas a matsayin butulu da tayi anfani dasu wajen yakin neman zabe da alkawarin sassauta dokar amma kuma yanzu ta saka masu da tsananta dokar.

Malam Isa Mani daya daga cikin shugabannin 'yan asalin arewa masu sana'ar achaba ko okada yace gaskiya gwamnatin bata yi masu adalci ba yace lokacin fafutikar zabe da tsohon gwamnan da sabon tare suke hawa suna kemfen.

Suna bukatar gwamnatin ta yi masu adalci su cigaba dayin aikinsu kamar yadda suka saba. Idan kuma za'a hanasu sai gwamnatin ta nema masu aikin yi. Idan da gwamnati ta samar masu da aikin yi babau yadda zasu yi sana'ar achaba ko okada.

Ga rahoton Babangida Jibril da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:17 0:00
Shiga Kai Tsaye

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG