Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Leo Sarkisian, Tsohon Ma'aikacin Muryar Amurka Ya Rasu Ya Na Da Shekara 97


Leo Sarkisian da matarsa Mary
Leo Sarkisian da matarsa Mary

Leo Sarkisian da yarasu yana da shekara 97 shi ya kirkiro shirin Muryar Amurka da ta dade yana dakon rahotanni akan wake-waken nahiyar Afirka

Leo Sarkisian, mutumin da ya kirkiro dadden shirin nan na Muryar Amurka da ke dakko rahotanni kan wake-wake a nahiyar Afrika da ake kira “Music Time In Africa” a turance ya rasu yana mai shekaru 97

Sarkisian, ya kwashe rabin karni yana tafiye-tafiye a sassan Afirka, yana sauraron kananan mawakan yana kuma dakko rahotonni kan wasanninsu.

Wadannan rahotannin, sun kasance tushen shirin da ya fi dadewa da ake watsawa da harshen Ingilishi a Muryar Amurka.

Shi dai Sarkisian, ya kwashe shekaru 47 yana tafiya tare da mai dakinsa Mary, wacce ya aura a shekarar 1949, tare ne kuma suka rika haduwa da dubban kananan mawakan Afirka, suka kuma fito da fasaharsu idon Duniya.

Tafiye-tafiyen da ya yi, ya sa ya zama jagora cikin masanan wakokin nahiyar.

A cewar Heather Maxwell, kwararriya a fannin wake-wake, wacce kuma ita ta gaji Sarkisian, fitaccen aikin da ya yi, shi ne na nadar wakokin mawakin nan na Najeriya, marigayi Fela Kuti, gabanin ya kirkiro nau’in kade-kaden gargajiya na “Afrobeat,” wanda shi ne ya sa ya yi fice a duniya.

A shekarar 2012 Leo Sarkisian ya yi ritaya, a lokacin yana mai shekaru 91.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG