Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

LIBERIA: George Weah Ya Samu Goyon Bayan Tsohon Kwamandan Mayakan Sa Kai a Zaben Shugaban Kasa Zagaye na Biyu


Prince Johnson, tsohon kwamandan mayakan sa kai a yakin basasan Liberia wanda yanzu ya goyi bayan George Weah a zaben shugaban kasa zagaye na biyu .

Prince Johnson tsohon kwamandan mayakan sa kai lokacin yakin basasan Liberia ya goyo bayan George Weah a zaben shugaban kasar da za'a yi nan gaba

Tsohon kwamandan mayakan sa-kai, wanda yanzu Sanata ne a majlaisar dattawan kasar Liberia, wato Prince Johnson, ya bayyana goyon bayansa ga tsohon fitaccen dan wasan kwallon kafar nan George Weah, a zaben shugaban kasar da za a sake a wata mai zuwa.

Akwai alamu, wannan goyon baya na Johnson ya taimakawa Weah lashe zaben wanda a wancan zagaye ya samu kashi 38.4 cikin 100 na kuri’un da aka kada a farkon watan nan, kason da ya fi na kowane dan takara, amma kuma ya gaza kai wa mizanin samun rinjayen kuri’un da ake bukata kafin a lashe zaben.

A ranar 7 ga watan Nuwamba, Weah zai kara da mataimakin shugaban kasar Joseph Boakai, wanda ya samu kashi 28.8 cikin 100 na kuri’un da aka kada a zaben ranar 10 ga watan Oktoba.

Shi dai Prince Johnson ya yi kaurin suna a matsayin kangararre a duk fadin duniya, wanda ya taba fitowa a wani faifan bidiyo yana kurbar giya yayin da yake kallo mutanensa suka kashe tsohon shugaban Liberia, Samuel Doe ta hanyar azabtarwa a shekarar 1990.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG