Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

LIBYA: Sojojin Amurka Sun Cafke Wanda Yake da Hannu a Kisan Jakadan Kasar a Benghazi


Shugaban Amurka Donald Trump

Shugaban kasar Amurka ya sanar cewa sojojin kasarsa sun cafke Al-Imam wanda ake kyautata zaton yana da hannu a kisan jakadan Amurka a Benghazi a shekarar 2012

Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya ce sojojin Amurka na musamman sun kama wani dan bindiga da ake zargi da hannu a mummunan harin da aka kai na shekarar 2012 akan karamin opishin jakadancin Amurka a Benghazi dake kasar Libya.

Trump ya ce shine ya bayar da izinin wani aiki da ya kai ga cafke mutumin mai suna Mustafa al-Imam a birnin Misrata, dake arewacin Libya.

Ya zuwa yanzu dai babu cikakken bayani kan wannan al’amarin, amma dai an san cewa shi Al-Imam yana hannun sojojin Amurka, kuma ana kan hanyar kawo shi Amurka don ya fuskanci shari’a.

Mayakan kungiyar ISIS ne suka kai harin ranar 11 ga watan Satumbar shekarar 2012 kan wani masaukin ma’aikatan jakadancin Amurka a wani gida a Banghazi, inda kuma aka hallaka har da shi kansa jakadan na Amurka Christopher Steven da wasu Amurkawa uku.

Harin ya haifar da wani dogon bincike da sauraron bahasi ga ‘yan Majalisun Amurka, kan cewa ko tsohuwar sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton da sauran manyan jami’an Amurka sunyi watsi da gargadin karfafa tsaro a ofishin jakadancin Amurka saboda kokarin gujewa faruwar tashin hankali.

Sai dai duk da zaman sauraron bahasin da aka yi ta yi, da dogon binciken da ‘yan Republican suka yi, ba a sami Clinton da ma’aikatarta da wani laifi ba.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG