Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Likitoci Na Cigaba da Yajin Aiki a Najeriya


Ministan Kiwon Lafiya na Najeriya, Dr. Isaac Folorunsho Adewole
Ministan Kiwon Lafiya na Najeriya, Dr. Isaac Folorunsho Adewole

Rahotanni daga Ibadan babban birnin jihar Oyo na nuni da cewa likitocin asibitin koyaswa ko UCH, asibitin koyaswa na farko a duk fadin kasar na cigaba da yajin aiki

Yau likitocin da ake kira Resident Doctors suka shiga rana ta biyu na yajin aikin da suka soma yi a duk fadin kasar.

A asibitin koyaswa dake Ibadan babban birnin jihar Oyo, wato UCH, likitocin wurin na cigaba da yajin aiki kamar sauran 'yanuwansu a kasar.

Shugaban kungiyar likitocin masu neman kwarewa a fannoni daban daban na kiwon lafiya ko Resident Doctors, Dr. Olusegun Olofa ya tabbatar cewa suna yajin aiki ne saboda gwamnati ta ki aiwatar da yarjejeniyar da suka kulla tun shekarar 2013 har zuwa yau.

A cewarsa a watan Yuli sun ba gwamnati sanarwar zuwa yajin aiki idan ba'a biya masu bukatunsu ba a karshen kwanaki 21 daga ranar sanarwar. Da lokaci ya kure sun kara bada kwanaki bakwai amma shiru ka ke ji kamar an shuka dusa. Inji shugaban sai ranar da suka fara yajin aiki ne gwamnati ta waiwayesu.

Likitocin na neman gwamnati ta biyasu cikakken albashi kamar sauran ma'aikatan kiwon lafiya a asibitoci da gwamnatin take biya..

Ga rahoton Hassan Umar Tambuwal da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:45 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG