Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Likitoci Sun Kai Karar Ma'aikatar Kiwon Lafiya a Nijar


A Jamhuriyar Nijar, kungiyar likitoci masu kwarewa ta musamman ta shigar da kara a gaban hukumar yaki da cin hanci ta kasar domin ta binciki cuwacuwar da ake zargin ta yi katutu a ma’aikatar kiwon lafiyar kasar.

A taron manema labaran da suka kira, kwararrun likitoci magoya bayan kungiyar ‘SMES’ sun yi tir da abin da suka kira take-taken hukumomin kiwon lafiya sakamakon tursasawar da suka ce ana yi wa abokan aikinsu a nan Nijar kamar yadda abin ya faru a baya -ayan nan da wata kwararriyar likitar cutar daji, Dr. Dille Issimouha.

Dr. Nafissa Naneito kusa ce a kungiyar kwararrun likitocin, ta kuma ce ana kumbiya-kumbiya wajen fitar da kudaden da ake biya da ake fitar da marasa lafiya ‘yan Nijar kasar waje domin neman magani.

Sakataren Kungiyar ta SMES, Dr. Zabeirou Kongouize, ya ce tuni dai kungiyar ta shigar da kara a gaban hukumar yaki da cin hanci ta HALCIA domin ta binciki wannan al’amari.

A karon farko, tun bayan tasowar wannan takaddama, ofishin Ministan Kiwon Lafiyar Al’umma, ya maida martani ta hanyar taron manema labaran da Magatakardan Ministan, Abache Ranao, ya kira a jiya Laraba.

Yanzu dai hankalin ‘yan Nijar ya karkata wajen hukumar yaki da cin hanci ta HALCIA domin jin abubuwan da rahoton bincikenta zai kunsa.

Saurari cikakken rahoton Souley Moumouni Barma daga Yamai:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:34 0:00


Facebook Forum

XS
SM
MD
LG