Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Lilin Baba Ya Saki Sabon Kundin Wakoki


Lilin Baba
Lilin Baba

Fitaccen mawakin Hausa na zamani, Lilin Baba ya saki wani sabon kundi mai dauke da wakoki 14 wanda ya mai take da “Sounds From the North,” wato sautuka daga arewa.

Kundin ya hada har da Allah-koron waka hudu.

Ya saki kundin ne a ranar Litinin, wanda ya gayyato shahararrun mawakan zamani da suka taya shi rera wakoki, wadanda suka hada da Adam A Zango, Umar M. Shareef, Ali Jitta, Soja Boy da kuma Bangis.

Lilin Baba wanda ya da waokokinsa irinsu “In Da Dadi,” ya saki wakoki a wannan kundi, wadanda suka hada da “Ahaiyye,” “Ba Wata,” da “Dan Mama.”

Sauran sun hada da “Overload” wacce ya gayyaci Adam A. Zango da “Farida” da ya gayyato Ali Jitta.

“Gobe ne fah, ubangiji Allah ya ba da sa’a” Lilin Baba wanda har Ila yau ya yi face da wakokin "Tsaya" da "Inda Inda," ya rubuta a shafinsa na Instagram a ranar jajiberin fitar da kundin.

Wakokin Allah-koron sun hada da “Awarwaro” “Voom,” “Tsaya” da kuma “In Da Dadi.”

Bidiyo

Saurari Dalilin Da Ya Sa Ummi Zeezee Ta Ce Tana So Ta Kashe Kanta A Hira Da Wakiliyar VOA Baraka Bashir
please wait

No media source currently available

0:00 0:06:39 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

VOA CASU

VOA CASU: Saurari Bayanin Jarumar Kannywood, Nafeesa Abdullahi
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:24 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

VOA CASU

VOA CASU: Bikin Yini Na Auren Zawarawa A Kano
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG