Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Liverpool Na Zawarcin Mbappe, Dortmund Ta Katsewa Masu Zawarcin Haaland Hanzari


Kylian Mbappe

Mbappe na daga cikin fitattun ‘yan wasan kwallon kafa na duniya da aka fi nema, kuma ga dukkan alamu kakar dan wasan mai shekara 22, ta kusa yanke saka.

Rahotanni na nuni da cewa, mai yiwuwa Liverpool ta yi zarra a tsakanin masu zawarcin dan wasan PSG Kylian Mbappe.

Mbape na daga cikin fitattun ‘yan wasan kwallon kafa na duniya da aka fi nema, kuma ga dukkan alamu kakar dan wasan mai shekara 22, ta kusa yanke saka.

Liverpool da Real Madrid na daga cikin masu sha’awar ganin sun sayi dan wasan, amma shugaban Madrid Florentino Perez ya bayyana matsalar kudade da kungiyarsa ta shiga.

Hakan ya sa masu lura da al’amuran kwallon kafa suke ganin karshenta, Mbappe wanda dan asalin Faransa ne ya nufi Anfield.

A daya gefen kuma Borussia Dortmund ta katsewa masu zarwacin dan wasanta Erling Haaland hanzari, inda ta ce dan wasan zai ci gaba da zama a kungiyar har karshen kakar wasa mai zuwa.

Rahotannin da dama sun nuna cewa kungiyoyin gasar Premeir da dama na neman Haaland, cikinsu har da Manchster United da Manchester City.

Bayanai sun yi nuni da cewa, dan wasan na da kudi euro miliyan 75 akansa a kwangilar da ya rattaba hannu da Dortmund.

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG