Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Lukaku Ya Sake Bude Taskar Kwallayensa A Chelsea


Lukaku a lokacin da yana murnar zura kwallonsa

Dan shekara 28, Lukaku ya zura kwallonsa ne a minti na 15 da fara wasa, sannan Reece James ya biyo da kwallo ta biyu a minti na 35.

Sabon dan wasan Chelsea Rumelu Lukaka da ya yi kome, ya zura kwallonsa ta farko a kungiyar ta ‘Blues’ a karawar da suka yi da Arsenal a gasar Premier ta Ingila.

Chelsea ta doke Arsenal da ci 2-0 a wannan karawa wacce aka buga a filin wasa na Emirates a ranar Lahadi.

Dan shekara 28, Lukaku ya zura kwallonsa ne a minti na 15 da fara wasa, sannan Reece James ya biyo da kwallo ta biyu a minti na 35.

Lukaku lokacin da yake fafatawa da 'yan Wasan Arsenal
Lukaku lokacin da yake fafatawa da 'yan Wasan Arsenal

Arsenal ta samu damar fenariti a lokacin da aka kada Bukayo Saka amma alkalin wasa bai amince ba.

Kungiyar ta sayo Lukaku akan kudi fam miliyan 97.5, wannan kuma shi ne karo na biyu yake zuwa ya bugawa kungiyar wasa daga Inter Milan wacce ta saye shi a 2019.

Dan asalin kasar Belgium, Lukaku shi ne dan wasa kwallon kafa na bakwai cikin jerin ‘yan wasan da aka yi cefanan su.

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG